
Sheikh Isa Ali Pantami, tsohon ministan sadarwa, ya yi ta’aziyya ga iyalan malamin addinin musulunci, Dr. Idris Abdul’Azeez Dutsen Tanshi, wanda ya rasu a daren Juma’a, 6 ga watan Shawwal, 1446AH, bayan fama da jinya.
Pantami ya bayyana alhinin sa a shafinsa na Facebook, inda ya roki Allah ya jiƙansa, ya gafarta masa kura-kuransa, tare da addu’ar Allah ya sa shi a Aljanna. Ya ce: “Inna lil Laahi wa inna ilaiHi Raaji’un! Muna mika ta’aziyyar rasuwar Dr. Idris Abdul’Azeez zuwa ga iyalansa da yan’uwansa.”
Rahotanni sun tabbatar da cewa Dr. Idris ya shafe lokaci yana fama da jinya kafin rasuwarsa, wanda ya tilasta masa dakatar da karatuttukansa da huduba a masallacin Juma’a a garin Dutsen-Tanshi.
Ana sa ran za a yi masa jana’iza yau, 4 ga watan Afrilu, 2025, da misalin karfe 10:00 na safiya a Bauchi.