NLC Ta Jaddada Bukatar Inganta Rayuwar Ƴan Najeriya a 2025

Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta fitar da sanarwa mai mahimmanci kan abubuwan da ya kamata gwamnati ta mayar da hankali a kai a shekarar 2025. Shugaban ƙungiyar, Joe Ajaero, ya yi kira ga dukkan gwamnatoci su ba da fifiko ga walwala da jin daɗin ƴan Najeriya.

A cikin sanarwar, NLC ta yi nuni da cewa akwai bukatar a janye kuɗirin harajin da aka gabatar a gaban majalisar tarayya. Ajaero ya bayyana cewa, “Mulki yana bukatar ya kasance abin amfani ga jama’a,” yana mai jaddada cewa jindadin ƴan kasa shine muhimmin dalilin kasancewar kowace gwamnati.

Ƙungiyar ta kuma ce, ya kamata gwamnati ta tabbatar da cewa akwai ingantaccen abinci, kiwon lafiya, ilimi, da tsaro a cikin al’umma. NLC ta yi nuni da cewa, “Dole ne manufofin gwamnati su nuna gaskiya, adalci, da haɗa kai.”

A cikin wannan sanarwa, NLC ta bayyana damuwarta kan ƙarancin kuɗi da ƴan Najeriya ke fuskanta, tare da bukatar gwamnati ta gaggauta nemo mafita akan wannan matsala.