
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ta bayyana hasashen cewa za a samu ruwan sama a wasu jihohi shida na Kudancin Najeriya daga ranar 9 zuwa 11 ga watan Afrilu. Jihohin da za su fuskanci ruwan sama mai karfi sun haɗa da Edo, Akwa Ibom, Bayelsa, Delta, Ogun, da Cross River.
Hukumar ta gargadi mutane kan yiwuwar ambaliya a sassan da ruwan zai sauka. An kuma yi gargadi kan tuki a lokacin ruwan sama domin kauce wa hadari. NiMet ta bayar da shawarar cewa mutane su guji hanyoyi masu santsi da kuma tsayar da na’urorin lantarki kafin ruwan sama ya sauka.
Hukumar ta bayyana cewa wasu jihohi za su fuskanci yayyafi, yayin da wasu ba za su samu ruwan sama ba a cikin kwanakin ukun. An yi kira ga jama’a su kasance a cikin shiri domin gujewa duk wani abu da zai iya haifar da hadari.