
Gwamnatin tarayya ta Najeriya, karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu, ta sanar da sayen jiragen yaki kirar Alpha Jets guda 12 daga kasar Faransa. Wannan mataki na nufin karfafa rundunar sojin saman Najeriya domin yaki da ƴan bindiga da ke ta’azzara a wasu sassan kasar.
Hafsan Sojin Saman Najeriya (CAS), Hassan Abubakar, ya bayyana hakan a taron horo da bita kan tsaro da aka gudanar a Abuja. Ya ce an sayo jiragen yaki ne ta hanyar kamfanin SOFEMA, wanda ke gudanar da sayen kayan aikin soji daga kasashen waje.
CAS Hassan Abubakar ya jaddada cewa jiragen Alpha Jets suna da tasiri wajen gudanar da ayyukan sojin saman Najeriya, musamman wajen daukar makamai da kai harin kusa. Haka zalika, ya bayyana cewa za a kawo wasu jiragen yaki kirar M-346FA da T-129, tare da jiragen saukar angulu guda biyu a cikin wannan shiri.
A cewar Abubakar, “A shekara mai zuwa, NAF za ta karbi jiragen yaki kirar M-346FA guda 24 da jiragen saukar angulu kirar AW-109 guda 10.” Wannan mataki na sayen jiragen yaki ya zo ne a lokacin da Najeriya ke fuskantar kalubale daga ƴan bindiga da sauran kungiyoyi masu tayar da hankali a cikin kasar.
Olusegun Dada, mataimakin na musamman ga shugaban kasa, ya tabbatar da cewa an kammala shirye-shiryen jigilar dukkanin jiragen. Ya bayyana cewa wannan sayen jiragen yaki na daga cikin manufofin gwamnatin Tinubu na inganta tsaro a Najeriya.
Jiragen Alpha Jets sun kasance suna da tasiri wajen yaki da ƙungiyoyin ta’addanci da sauran barazanar tsaro a Najeriya. Wannan mataki na gwamnatin na iya zama alama ta kyautata tsaro da kuma rage tasirin ƴan bindiga a kasar.