
Babban Hafsan Tsaro na Najeriya, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta sayo sabbin makamai masu inganci domin yaki da hare-haren Boko Haram, ISWAP, da sauran yan ta’adda. A yayin ziyarar da ya kai jihar Borno, Janar Musa ya tabbatar da cewa sabbin makaman suna da inganci sosai kuma za a fara amfani da su cikin gaggawa.
Ya jaddada cewa gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na da kwarin gwiwa wajen dawo da zaman lafiya a kasar. CDS Musa ya roki ‘yan Najeriya su ba da hadin kai ga sojoji a wannan yaki da ta’addanci, yana mai cewa tsaro aiki ne na kowa da kowa.
Janar Musa ya ce, “Matsin lambar da ake yi wa yan ta’adda a yankin Sahel na kara jawo musu hare-hare a Najeriya, amma muna aiki tuƙuru domin magance wannan matsala.”
Haka zalika, ya yi kira ga ‘yan Najeriya su kasance masu kiyaye tsaro, yana mai nuna cewa sojoji na kan lamarin kuma ba su fargaba ko kadan. Wannan sabuwar mataki na sayen makamai na nuni da himmar gwamnatin Najeriya na kawo karshen tashin hankali da hare-hare a cikin kasar.