
Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa ba za ta karɓi ‘yan Venezuela da Amurka ke shirin mayarwa ba, musamman wadanda ke cikin kurkuku. Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa Najeriya na fama da nata matsaloli da ba za ta karbi na wasu kasashe ba.
A wata hira da aka yi da shi a shirin Channels TV, Tuggar ya ce Najeriya tana da al’amuran da take kula da su, kuma ba za ta zama wurin ajiye fursunonin wata kasa ba. Ya jaddada cewa Najeriya ba za ta rungumi shirin da wasu kasashen ke yi na mayar da ‘yan gudun hijira ko fursunoni daga kasashen waje ba.
Ministan ya bayyana cewa, “Amurka na matsa lamba ga kasashen Afirka da su karɓi wasu ‘yan Venezuela da suke shirin korar su, ciki har da wadanda ke fitowa daga gidajen yari. Wannan ba abu ne da zai yiwu ba.”
Hakanan, Tuggar ya yi bayani kan tattaunawar da Najeriya ke yi da gwamnatin Amurka kan sabon tsarin biza da ya takaita lokacin zaman ‘yan Najeriya a Amurka. Ya kuma bayyana takaici kan matakin da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta dauka na hana wasu ‘yan Najeriya biza.
Wannan al’amari ya jawo cece-kuce a cikin al’umma, inda ake ta tattaunawa kan matsayin Najeriya da kuma tasirin wannan shiri na Amurka. Gwamnatin Najeriya ta yi nuni da cewa tana da nauyin kula da tsaro da walwalar jama’ar ta, don haka ba za ta yarda ta zama wurin kwashe matsalolin wasu kasashe ba.