Wednesday, April 30Labarai Masu Muhimmanci

Na Gaji da Rayuwar Nan”: Ƴar Marigayi Ado Bayero Na Barazanar Halaka Kanta

Zainab Ado Bayero, ɗiyar marigayi sarkin Kano, Ado Bayero, ta bayyana mawuyacin halin da take ciki tun bayan rasuwar mahaifinta. A cikin wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta, Zainab ta roki gwamnati da sarkin Kano na yanzu, amma ta ce ba a dauki mataki ba, tana barazanar kawo karshen rayuwarta.

Zainab ta bayyana cewa tana cikin damuwa a Legas, ba tare da tallafi ko kayan more rayuwa ba. Ta nuna cewa mahaifinta ya rasu ya bar ta ba tare da ilimi ko muhalli ba, kuma babu wanda ya damu da halin da take ciki.

A cikin bidiyon, Zainab ta ce: “Na gaji da rayuwar wahala. Ina jin tamkar babu wanda ya damu idan na rayu ko na mutu.” Ta yi ikirarin cewa duk kokarin da ta yi na neman taimako daga gwamnati da shugabanni, ba a amsa bukatunta.

Zainab ta koka kan cewa tana fuskantar barazanar korar ta daga gida tare da mahaifiyarta da kaninta, saboda rashin biyan kudin haya. Wannan yanayi na damuwa yana jawo hankalin masu ruwa da tsaki kan bukatar daukar matakin gaggawa don tallafawa mata da sauran wadanda ke cikin irin wannan hali.