Mustapha Naburaska Ya Bayyana Dalilin Komawarsa APC

Fitaccen dan wasan kwaikwayo na Kannywood, Mustapha Naburaska, ya bayyana dalilan da suka sa ya ajiye jar hular sa a jam’iyyar NNPP, tare da komawa jam’iyyar APC. A wata hira da DCL Hausa ta yi da shi, Naburaska ya musanta zargin cewa an samu sabani ko rikici a tsakanin sa da jam’iyyar Kwankwasiyya.

Naburaska ya bayyana cewa ya koma APC a inuwar Barau I Jibrin domin biyan bukatun kasuwancin sa da kuma samun ci gaba. Ya ce, da shigar sa APC, ya samu damar tallata manufofin gwamnati da kuma samun sabon mukami a cikin jam’iyyar.

Dan wasan ya bayyana cewa Sanata Ibrahim Lamido, wanda ke wakiltar Sakkwato ta Gabas, ne ya ja shi cikin tawagar Barau I Jibrin. Ya bayyana cewa wannan mataki ya ba shi damar samun sabbin damar aiki da kuma inganta harkokin kasuwancinsa.

“Idan aka ce za a yi aiki, za a ba ka wani yanki da za ka ci gaba da harkokinka. Ba yana nufin za ka bar wani ka koma wajen wani ba ne,” in ji Naburaska. Ya ci gaba da cewa, ya samu tagomashin kwangila daga kamfaninsa wanda ke tallata al’amuran da suka shafi kasa, wanda ya sa ya rungumi tafiyar Barau.

Sai dai, Naburaska ya nanata cewa zai ci gaba da mutunta Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir Yusuf, duk da cewa ba a ba shi mukamin da ya rike a gwamnatin Kwankwasiyya ba. Ya ce, ya zabi komawa APC domin samun canjin da yake bukata.

A halin yanzu, wasu shahararrun ‘yan wasan Kannywood sun kuma bayyana ficewar su daga jam’iyyar NNPP zuwa APC, lamarin da ke nuna sauyin lamuran siyasa a jihar Kano.