
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta yanke wa shahararriyar jarumar TikTok, Murja Ibrahim Kunya, hukuncin daurin watanni shida a gidan yari ko kuma biyan tarar Naira dubu hamsin (N50,000) bayan samunta da laifin likin kudi da kuma tattake su a wani otel a Kano.
Mai Shari’a Simone Amobeda ne ya yanke wannan hukunci bayan Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC) ta gurfanar da Murja Kunya a gaban kotun bisa laifin karya sashe na 21(1) na dokar Babban Bankin Najeriya (CBN) ta shekarar 2007. An kama Murja Kunya ne a watan Disambar 2023 bayan wani bidiyo da ya nuna ta tana likin kudi da tattake su a wani shagali da aka yi a Otal din Guest Palace da ke Kano ya bazu a shafukan sada zumunta.
EFCC ta sha fama wajen kama Murja Kunya bayan ta tsere lokacin da aka fara neman ta ruwa a jallo. Sai a watan Maris din 2025 aka sake kama ta bayan makonni na bincike da sa ido. A ranar 20 ga Mayu, 2025 ne aka gurfanar da ita a gaban kotu inda ta amsa laifin da ake tuhumarta da shi.
Baya ga hukuncin daurin ko tarar, Mai Shari’a Amobeda ya kuma bayar da umarnin a nada Murja Kunya a matsayin jakadiyar CBN da EFCC domin wayar da kan jama’a game da illolin wulakanta takardun kudi. Alkalin ya ce ya yi fatan wannan hukunci zai zama izina ga sauran masu amfani da shafukan sada zumunta da su guji aikata irin wannan laifi. Wannan hukunci dai shi ne irinsa na farko da aka yanke wa wani fitacce a shafukan sada zumunta dangane da wulakanta kudin Najeriya.