Mummunan Hali: ‘Yan Bindiga na Ciyar da Karnuka da Jariran da Aka Haifa


Dan majalisar wakilai daga Zamfara, Aminu Jaji, ya bayyana mummunan lamari da ke faruwa a yankin. Ya ce ‘yan bindiga suna ba karnukansu jariran da aka haifa a cikin daji, wani abin da ya janyo fargaba a tsakanin al’umma.

Jaji ya bayyana cewa wata mata da aka sace ta haihu a daji, inda shugaban ‘yan bindigar ya jefar da jariran ga karnukansa, suka kuma ci su. Wannan lamari ya jawo kiran gaggawa ga gwamnati domin daukar matakai masu inganci don tabbatar da tsaro a wannan yanki.

Dan majalisar ya ce akwai bukatar amfani da sabbin fasahohi da kayan aiki don yakar ‘yan ta’adda, yana mai cewa sojojin Najeriya na da karfin da zai ba su damar tinkarar wannan matsala idan aka ba su goyon baya.

Hakanan, Jaji ya bayyana cewa a mazabarsa kadai, ‘yan bindiga sun sace fiye da mutum 200, yana mai kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya inganta tsaro a Arewa ta Yamma.

Matsalar tsaro a Zamfara na ci gaba da tsananta, tare da al’ummar yankin suna fuskantar barazana daga ‘yan bindiga da ke kai hare-hare a kai a kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *