Miyagun Ƴan Bindiga Sun Sace Malaman Coci a Jihar Adamawa

Rundunar ƴan sanda ta jihar Adamawa ta tabbatar da sace malaman cocin EYN guda biyu a ranar Lahadi da ta gabata. An sace limamin cocin, Rabaran James Kwayang, tare da sakataren sa, Rabaran Ishaku Chiwar, a garin Mbila-Malibu a karamar hukumar Song.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sandan, SP Suleiman Nguroje, ya bayyana cewa an tura dakaru domin ceto limaman cikin koshin lafiya. Ya ce an yi garkuwa da malaman ne da misalin karfe 11 na dare.

Shugaban cocin EYN, Rabaran Daniel Mbaya, ya yi kira ga al’umma da su yi addu’a a kan hakan, yana mai rokon jami’an tsaro da su dauki matakan gaggawa don ganin an sako fastocin lafiya. Ya bayyana cewa wannan lamari ya tayar da hankalin jama’a, don haka yana bukatar goyon bayan addu’o’i daga mabiya cocin EYN da sauran ƴan Najeriya.

Rabaran Daniel ya ce: “Muna kira ga ƴan Najeriya da su taimaka mana da addu’o’i don Allah ya kubutar da waɗannan mutane biyu da kuma ba iyalansu karfin jure wannan hali.” Wannan lamari ya jawo hankali sosai a jihar Adamawa, tare da fatan ganin an ceto malaman da aka sace cikin sauri.