
Mijin Senator Natasha Akpoti-Uduaghan, Emmanuel Uduaghan, ya yi magana kan zargin da matarsa ta yi wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, na aikata abubuwan da ba su dace ba. Uduaghan, wanda shima babban mutum ne a masarautar Warri a Jihar Delta, ya bayyana cewa matar tasa ta bayyana masa duk abubuwan da suka faru a tsakaninta da Akpabio.
A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Asabar, Uduaghan ya ce ya yi ƙoƙarin shawo kan al’amarin cikin ladabi da girmamawa, tare da fatan samun sulhu. Ya ce ya yi tunanin Akpabio aboki Kuma Dan uwa, don haka ya nemi ganawa da shi don tattauna damuwar matarsa.
Uduaghan ya ce, “Matar ta bayyana mini duk wani abu da ya shafi Shugaban Majalisar Dattawa, wanda na dauka a matsayin aboki Kuma Dan uwa. Na yi ƙoƙarin magance al’amarin da kyau da hakuri, saboda wannan shine aikina a matsayin shugaban gargajiya.”
Ya kuma bayyana cewa a lokacin ganawarsu, ya nemi Akpabio ya girmama matarsa, wanda take a matsayin sanata, tare da mutunta abokantakar da ke tsakaninsu. Duk da haka, Uduaghan ya nuna cewa matarsa ta ci gaba da bayyana damuwarta kan ci gaba da tsangwama daga Akpabio, wanda ya nuna cewa al’amarin ba a warware shi ba.
Senator Natasha ta zargi Akpabio a cikin wata hira da Arise Television, inda ta ce ya yi mata wasu abubuwa da ba su dace ba a lokacin da ta ziyarci gidansa a Uyo, Jihar Akwa Ibom, a ranar 8 ga Disamba, 2023. Ta zargi Akpabio da jawo ta da hannu da kuma yi mata wasu maganganu na jima’i a gaban mijinta.
A gefe guda, matan Akpabio, Ekaette, ta musanta zargin tare da shigar da kara guda biyu na zarginsa da bata suna, inda ta nemi Naira biliyan 350 a matsayin diyya ga mummunan suna da mijinta ya sha.
Duk da wannan rikicin, Uduaghan ya bayyana cewa yana da cikakken imani da amincin matarsa, yana mai cewa, “Ba zan taɓa musanya ta da komai ba, tana da matukar muhimmanci a rayuwata.” Ya kuma roki Majalisar Najeriya da ta duba lamarin cikin girmamawa da adalci yayin da hukumomin da suka dace ke gudanar da bincike.