
Fitaccen mawaki Innocent Idibia, wanda aka fi sani da 2Baba, ya yi matukar jawo hankali bayan ya nemi auren ƴar majalisar jihar Edo, Natasha Osawaru. Wannan lamari ya faru ne a cikin wani faifan bidiyo da ya bazu a kafofin sada zumunta, inda aka ga su suna rawa tare da jin dadin juna.
A bidiyon, 2Baba ya durkusa ya miƙa mata zoben neman aure, wanda ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin masoya da magoya bayan su. Natasha ta amince da auren, wanda ya tabbatar da soyayyar da ke tsakanin su. Wannan ya biyo bayan sanarwar rabuwa da mawaki ya yi da tsohuwar matarsa, Annie Idibia, kimanin kwanaki 17 da suka gabata.
Mawakin ya bayyana cewa Natasha tana da kima da basira, kuma ya ƙara da cewa ba ta da hannu a cikin matsalolin da suka shafi aurensa da Annie. Hakan ya jawo martani daga mabiya kafafen sada zumunta, inda wasu suka yaba masa, yayin da wasu suka yi tsokaci mai zafi kan wannan sabon al’amari.
Duk da haka, mutane na jiran matakin da za su dauka a wannan sabuwar alaka da mawaki da ƴar majalisar, yayin da suka bayyana sha’awar su ga zaman lafiyar wannan sabuwar soyayya.