
A ranar Talata, Ministan Makamashi, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba ta samu ingantacciyar mafita ga matsalar faduwar turakun wutar lantarki ba. A cewarsa, wannan matsala ta zama babban barazana ga tattalin arzikin Najeriya, inda ta haddasa faduwar turakun wuta sau da yawa a cikin shekarar 2024.
A yayin da yake bayani a gaban majalisar wakilai, Adelabu ya musanta rahoton da ke cewa turakun wutar lantarki sun fadi sau 12 a shekarar da ta gabata, yana mai cewa haka ma ba a tabbatar da cewa wannan matsala za ta ci gaba a 2025. Ya yi nuni da cewa magance wannan matsala yana bukatar haɗin kai daga hukumomin tsaro don hana lalata kayan wutar lantarki da kuma inganta kayayyakin da ake bukata.
Ministan ya bayyana cewa, duk da cewa ba za a iya kawo ƙarshen matsalar ba, gwamnatin za ta yi iya kokarinta wajen rage faduwar turakun. Ya kuma bayyana cewa ma’aikatar na aiki tare da hukumomin tsaro domin shawo kan wannan matsala, don tabbatar da cewa tsarin wutar lantarki na aiki yadda ya kamata.
Hakan na zuwa ne a lokacin da Najeriya, musamman Arewacin kasar, ke fuskantar matsanancin rashin wutar lantarki, wanda ya jawo asarar kudi da dama a shekarar 2024. Al’ummar Najeriya na fatan ganin ingantaccen tsarin wutar lantarki da zai kawo canji a rayuwar su.