Matawalle Ya Ja Kunnen Masu Sukar Tinubu, Ya Bayyana Amfanin Kudirin Haraji

Ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya bayyana cewa manufofin Shugaba Bola Tinubu kan tattalin arziki sun fara haifar da sakamako mai kyau. Matawalle ya jaddada goyon bayansa ga ƙudirin haraji, wanda ya bayyana a matsayin mai amfani wajen bunkasa tattalin arzikin ƙasar nan.

A cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na ma’aikatar tsaro, Henshaw Ogubike, ya fitar, Matawalle ya bayyana cewa tsare-tsaren da aka ƙaddamar na gyara fasalin haraji suna farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar. Ya ƙara da cewa, nan gaba kaɗan, ƴan Najeriya za su amfana daga waɗannan canje-canje.

Matawalle ya yi kira ga masu sukar gwamnatin Tinubu, musamman daga Arewa, da su riƙa bayyana gaskiya a cikin sukar da suke yi. A cewarsa, “Ina kira ga masu sukar su kasance masu faɗin gaskiya a cikin bayanansu.”

Dangane da ƙudirin haraji, Matawalle ya bayyana cewa wannan tsarin na da matuƙar muhimmanci domin inganta tsarin kuɗaɗen shiga ga gwamnati, tare da sauƙaƙa wa talakawa da ƙananan ƴan kasuwa. Ya bayyana cewa, gyaran haraji zai ƙara yawan kuɗaɗen shiga ga gwamnati da samar da ayyukan yi a sassa daban-daban.

Wannan jawabi na Matawalle ya zo ne a lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan ƙudirin haraji da aka gabatar a majalisun ƙasa, wanda ke da nufin inganta tattalin arzikin Najeriya.