Matasan Neja Delta Sun Goyon Bayan Haɗin Gwiwar Peter Obi da Gwamna Bala

Matasan yankin Neja Delta na Kudancin Najeriya sun bayyana goyon bayansu ga shirin haɗin gwiwar Peter Obi da Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi, a matsayin wani muhimmin mataki na kawo canji a siyasar Najeriya. Wannan goyon baya ya fito daga kungiyar matasan yankin, wato Neja Delta Youth Council (NDYC).

Shugaban NDYC, Israel Uwejeyan, ya bayyana cewa haɗin gwiwar Obi da Gwamna Bala na da matukar amfani ga ci gaban Najeriya, duba da kwarewar da kowanne daga cikinsu ya samu a harkokin shugabanci. Ya bayyana cewa wannan haɗaka ta na da burin tabbatar da hadin kai da kuma kawo sauyi mai ma’ana a cikin al’umma.

Uwejeyan ya jaddada cewa Gwamna Bala ya kasance mai himma wajen ganin an inganta haɗin kan ƙasa, yayin da Peter Obi ya zama abin misali a fannin shugabanci da tattalin arziki. Kungiyar ta bayyana cewa hadin kan wadannan shugabanni biyu na iya zama babban haske ga Najeriya a gabanin zaɓen 2027.

NDYC ta yi kira ga matasa da dukkanin ƴan Najeriya da su marawa wannan sabon yunƙuri baya, a matsayin wani abu da zai taimaka wajen gyara al’amuran ƙasar. Sun bayyana cewa lokaci ya yi da Najeriya za ta sami shugabanci nagari da ke da hangen nesa da kuma kishin jama’a.

A karshe, kungiyar ta yi tsokaci kan cewa haɗin kan Peter Obi da Gwamna Bala zai ba da damar samun sabbin ra’ayoyi da hanyoyi na inganta rayuwar al’umma, wanda hakan zai kawo ci gaba mai dorewa a cikin ƙasar.