
Kungiyar matasa da suka ci gajiyar shirin N-Power ta shirya gudanar da zanga-zanga kan basukan da suke bin gwamnatin tarayya. Matasan sun nuna damuwa kan yadda gwamnatin ta ki biyansu hakkokinsu na watanni tara duk da kokarin shawo kan lamarin.
Shugaban kungiyar, Kwamred Muhammad Abubakar Habibu GMB, ya bayyana hakan Yana Mai cewa sun yanke shawarar fara zanga-zanga daga ranar 2 zuwa 6 ga watan Disambar 2024 a birnin Abuja.
“Wannan kungiya tana wakiltar matasan N-Power da aka rike musu kudinsu na tsawon watanni takwas zuwa tara duk da kokarin nemo hanyoyin shawo kan lamarin amma ba a samu biyan bukata ba,” in ji Kwamred GMB.
Ya kara da cewa, “Duba da rashin samun biyan bukata, mun yanke shawarar fara zanga-zanga daga ranar 2 zuwa 6 ga watan Disambar 2024 daga Majalisar Tarayya zuwa ma’aikatar jin kai da walwala har zuwa ofishin kungiyar yan jaridu ta NUJ.”
“Za a fara gudanar da zanga-zangar da misalin karfe 10.00 na safe zuwa karfe 2.00 na rana.”
Wani da ya ci gajiyar shirin N-Power, Musa Muhammad Adamu, ya ce shi ma yana daga cikin masu bin gwamnatin basukan watanni takwas amma har yanzu shiru. Ya yabawa shugabannin kungiyar inda ya ce suna yi musu fatan alheri da samun abin ake bukata.
A baya, an fara ƙoƙarin ganin gwamnatin tarayya ta biya bashin da matasan Najeriya yan N-Power suka biyo gwamnatin da ta gabata. Tawaga da ta hada da bangarorin gwamnati da yan N-Power ta gana a birnin tarayya Abuja domin duba yadda za a biya matasan.
Wannan ya biyo bayan yin wani zama na musamman tsakanin matasan N-Power da wakilan gwamnatin tarayya a Abuja.