Matasan Arewa Sun Koka Kan Kudurin Gyaran Haraji na Tinubu

Kungiyar matasan Arewa a jihar Taraba ta bayyana adawarta ga sabuwar dokar haraji da kuma rufe iyakoki da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta gabatar. Matasan sun yi zargin cewa wannan kuduri yana bai wa yankin Kudu fifiko a kan Arewa, wanda hakan zai rage damar raya yankin Arewa da kuma inganta rayuwar al’umma.

Idris Ayuba, mai magana da yawun kungiyar, ya bayyana a taron manema labarai a Jalingo cewa sabuwar dokar haraji na da tasiri mai muni ga tattalin arzikin Arewa. Ya ce cire tallafin mai da rufe iyakokin suna kara tabarbarewar yanayin rayuwa a yankin.

Matasan sun yi kira ga Shugaba Tinubu da ya tabbatar da adalci wajen rabon arziki a kasar, tare da daukar matakan da zasu inganta cigaban Arewa. Sun bayyana cewa rashin kammala manyan ayyukan gwamnati, kamar Mambilla da hanyar Jalingo-Numan, na ci gaba da haifar da gibin ci gaban Arewa.

Kungiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi la’akari da tasirin manufofinta kan Arewa, tare da tabbatar da daidaito wajen raba arziki da inganta tattalin arzikin kasa. Wannan kira na matasan ya fito ne a cikin yanayi na rashin jin dadi da ke tsakanin al’umma a Arewa, wanda ke fuskantar matsaloli na tattalin arziki.