Malamin Addini Ya Hango Saukin Rayuwa a Najeriya a 2025

Malamin addini Samuel Ojo ya yi hasashen cewa shekarar 2025 za ta zama shekara ta kwanciyar hankali da ci gaban rayuwar ‘yan Najeriya. A cewar malamin, idan ‘yan Najeriya suka dage da addu’a da kyakkyawan yakini, to matsalolin tattalin arziki da rashin tsaro za su zama tarihi.

A yayin wani taron shekara-shekara da aka gudanar a garin Ori Oke Ogo da ke Ibadan, Ojo ya bayyana cewa Allah ya ji kukan da al’umma ke yi, kuma yanzu lokaci ne na sake gina kasa. Ya jaddada cewa akwai tarin alheri da zai zo a 2025, yana mai kira ga shugabannin kasar da su inganta tsare-tsaren da zasu kawo sauki ga talakawa.

Malamin ya bayyana cewa Najeriya na fama da wahalhalu da dama, ciki har da hauhawar farashin kayayyaki da rashin aikin yi, wanda ya jefa miliyoyin mutane cikin talauci. Duk da haka, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kasance masu kyakkyawan yakini, yana mai cewa matsalolin ba za su gagari Allah ba.

Fasto Samuel Ojo, wanda ya shahara a fannin hangen nesa da ayyukan taimakon al’umma, ya karfafa gwiwar al’umma da su ci gaba da addu’a da hadin kai domin samun saukin rayuwa a Najeriya.