Malamar Da Ta Haura Shekaru 20 Ta na Haurawa Rafi Domin yin Da’awa

An  bayyana labarin wata malama a Kano mai suna Khadija Muhammad, wacce ta shafe fiye da shekaru 21 tana haura rafi domin koyar da mata ilimin addini kyauta a kauyen Dan Shaye, karamar hukumar Rimin Gado. Wannan kyakkyawan aiki nata ya jawo hankalin jama’a, wanda hakan ya sa aka fara ba ta goyon baya da tallafi.

Malama Khadija ta bayyana cewa ta fara wannan aikin ne bayan ta ga bukatar taimako daga mata a kauyen, inda ta ke tsallake rafi kowanne lokaci domin kawo ilimin addinin Musulunci ga matan aure. Ta ce, “Wata kawata ta nemi taimakona don koyar da mata dokokin addinin musulunci, wanda zai inganta rayuwarsu.”

A halin yanzu, gwamnatin Kano ta fara daukar mataki tare da bayar da umarnin gina makarantar Sakandare a kauyen Dan Shaye, wanda hakan zai taimaka wajen inganta ilimi a wannan yanki. Hakan na zuwa ne bayan an gudanar da bincike da ya nuna rashin makarantu da asibitoci a kauyen.

Jama’ar Kano sun nuna godiya ga Malama Khadija bisa wannan sadaukarwar ta, inda kungiyoyi da dama suka fara neman hanyar tallafa mata. Kabiru Bello Tukur, wani dan jarida, ya bayyana cewa akwai wadanda suka dauki nauyin ba ta kudade domin taimakonta wajen gudanar da wannan aiki mai kyau, wanda hakan ya nuna yadda al’umma ke goyon bayan ta.

Malama Khadija ta ce, “Yanzu haka, akwai wanda ya dauki alkawarin bayar da N30,000 duk wata, wanda zai raba wa kowacce malama da ke zuwa N10,000.” Wannan tallafi na kudi da aka fara bayarwa yana taimakawa wajen rage nauyin da Malama Khadija ke dauka a wannan aikin.

A karshe, Malama Khadija ta yi kira ga gwamnati da ta ci gaba da tallafawa ilimi a kauyukan, musamman ma a wajen da ake da karancin makarantun sakandare, domin inganta rayuwar al’umma da kuma ilimin addini.