Majalisar Wakilai Ta Jinjina Ayyukan Sojojin Najeriya, Ta Fadi Hanyoyin Taimako

kwamitin majalisar wakilai kan harkokin sojoji ya bayyana goyon bayansa ga rundunar sojojin Najeriya, tare da jinjina wa ayyukan da suka yi a shekarar 2024 wajen yakar ta’addanci. Shugaban kwamitin, Aminu Balele, ya bayyana cewa majalisar ta gamsu da yadda aka aiwatar da kasafin kudin sojojin na wannan shekara, inda aka samu nasara fiye da kashi 99%.

A yayin ganawarsu da shugaban rundunar sojojin kasa, Olufemi Oluyede, Balele ya jaddada cewa majalisar za ta ci gaba da bayar da dukkan goyon bayan da ake bukata domin magance matsalar rashin tsaro a Najeriya. Ya ce, “Mu na goyon bayan sojojinmu ta fuskar tabbatar da hadin kai da aiki tare da dukkanin sauran sojojin kasar nan.”

Majalisar wakilai ta yaba da yadda sojojin Najeriya suka yi kokarin yakar ayyukan ta’addanci a fadin kasar, musamman a sabuwar shekara da muke ciki. Balele ya bayyana cewa kwamitin ya duba yadda aka aiwatar da kasafin kudin sojojin na 2024, kuma sun samu muhimman bayanai kan ayyukan da suka yi, tare da bukatar a kara ba su damar magance matsalolin tsaro da ke ciwa Najeriya tuwo.

Shugaban rundunar tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa talauci da yunwa na daga cikin abubuwan da ke ta’azzara matsalar ta’addanci a kasar. Ya yi kira ga hadin gwiwa daga kasashen duniya da kuma daga cikin gida domin samun nasarar yaki da kungiyar Boko Haram da sauran kungiyoyi masu tayar da hankali.

Majalisar wakilai ta yi alkawarin ci gaba da tallafawa sojojin Najeriya don tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duk fadin kasar, tare da fata cewa wannan goyon baya zai taimaka wajen samun nasarori a fannin yaki da ta’addanci.