
Majalisar Wakilai ta Najeriya ta amince da kudirin da ke neman cire kariya daga shari’a ga Mataimakin Shugaban Kasa, Gwamnoni da mataimakansu. Wannan kudiri, wanda Solomon Bob, dan majalisa daga jihar Rivers ne ya dauki nauyinsa, yana nufin hana rashawa da karfafa gaskiya a shugabanci.
Kudirin yana neman gyara Sashe na 308 na kundin tsarin mulki, wanda ke bayar da kariya ga wadannan shugabanni daga tuhuma ta shari’a yayin da suke kan mulki. Wannan mataki yana da nufin rage yawan cin hanci da rashawa a cikin gwamnati.
Haka zalika, Majalisar ta amince da kudirin da zai baiwa sarakuna matsayi a kundin mulki, tare da gyara tsarin mulkin kananan hukumomi da kirkirar sababbin jihohi. Sababbin jihohin da ake son kirkira sun hada da Oke-Ogun, Ijebu, Ife-Ijesa, Tiga a jihar Kano da Orlu da Etiti.
Wannan mataki na Majalisar ya zo ne a lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan yanda za a inganta tsarin mulki da kuma yakar cin hanci a Najeriya.