
Daga Abuja – Majalisar Dattawan Najeriya ta gudanar da zama inda ta bayar da shawarar cewa sojoji su haɗa kai da al’ummar yankunan da ke fama da hare-haren kungiyar yan ta’addan Lakurawa. Wannan shawarar ta biyo bayan mummunan hari da ƴan kungiyar suka kai a kauyen Mera a jihar Kebbi, wanda ya jawo asarar rayuka da dama.
Majalisar ta bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta daukar matakai na gaggawa don kawo karshen ayyukan kungiyar Lakurawa kafin ta mamaye sassan Arewa. Sanata Yahaya Abdullahi, daga Kebbi ta Arewa, ya gabatar da korafi game da matsalar a zaman, wanda ya jawo hankalin sauran sanatan.
A yayin muhawara, ‘yan majalisar sun yi kira ga rundunar sojojin Najeriya su yi aiki tare da mazauna yankunan da ake kai hare-hare, domin kafa tsare-tsare da za su taimaka wajen gano shirin ƴan ta’addan kafin su kai hari. Hakan na nufin cewa sojoji za su yi amfani da bayanan da al’umma za su bayar don inganta tsaron yankin.
Majalisar Dattawa ta yi gargaɗi cewa rashin daukar matakan da suka dace na iya barin kungiyar Lakurawa ta fadada ayyukanta a wasu sassan Najeriya. Haka zalika, ta bukaci gwamnatin tarayya ta tura tawaga zuwa yankin Kebbi domin tantance ɓarnar da aka yi a harin na baya-bayan nan.
A cikin makon da ya gabata, ƴan ta’addan Lakurawa sun kai hari a jihar Kebbi inda suka kashe sojoji takwas, wanda hakan ya jawo fargaba a tsakanin al’ummar yankin. Majalisar ta bukaci dakarun sojoji su kara kaimi wajen hana mummunar aƙidar kungiyar ta Lakurawa yaɗuwa a cikin al’umma.
Majalisar Dattawa ta yi fatan cewa tare da haɗin gwiwar sojoji da al’umma, za a iya dakile ayyukan ta’addanci da kawo zaman lafiya a yankunan da ake fama da hare-hare.