Wednesday, April 30Labarai Masu Muhimmanci

Majalisar Dattawa Ta Fadi Sirrin Amincewa da Kudirin Haraji na Tinubu

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa ‘yan Najeriya za su ji dadin ribar dimokuradiyya da zarar Majalisar Dokoki ta amince da kudirin haraji da gwamnatin tarayya ta gabatar. Wannan bayani ya fito ne a cikin sakon sabuwar shekara da Akpabio ya sanya wa hannu.

Sanata Akpabio ya bayyana cewa, wannan kudirin gyaran haraji zai zama muhimmin mataki wajen inganta tattalin arzikin Najeriya. Ya ce, “Daga cikin gyare-gyaren da gwamnatin nan ta kaddamar, ina tabbatar wa da ‘yan Najeriya cewa za mu fara jin dadin dimokuradiyya mai dorewa a wannan sabuwar shekara.”

Kazalika, Akpabio ya taya ‘yan Najeriya murnar sabuwar shekara, yana mai cewa shekarar 2025 za ta kawo arziki da kyakkyawan yanayi ga al’umma. Ya jaddada cewa, tare da hadin kai, za a iya kai Najeriya ga babban matsayi.

A cewar rahotannin, bayan amincewar da Majalisar Dokoki za ta yi, Shugaban Kasa Bola Tinubu zai rattaba hannu a kan kudirin, wanda ke da nufin inganta tsarin haraji da bunkasa tattalin arzikin kasa.

Akpabio ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi hakuri da kuma jure dukkan kalubalen da ke fuskantar kasar a yanzu, yana mai tabbatar da cewa gwamnati na aiki tukuru wajen kawo canji mai kyau ga al’umma.