
Majalisar wakilan Najeriya ta ki amincewa da kudurin da zai kara wa’adin shugaban kasa da gwamnoni zuwa shekara shida amma wa’adi daya kawai. Wannan shawarar ta zo ne bayan da majalisar ta yi zamanta a ranar Alhamis, 21 ga Nuwamba, 2024. A yayin zaman, yan majalisar sun yi fatali da kudurin.
Kudurin da aka yi watsi da shi na nufin zababben shugaban kasa da gwamna da shugabannin kananan hukumomi za su yi mulki sau daya na shekara shida kawai. Dan majalisa daga jihar Imo, Ikeagwuonu Ugochinyere da wasu yan majalisu 33 ne suka bijiro da kudurin a farkon wannan shekarar, da nufin samar da daidaito a tsarin mulkin kasar.
Amma a lokacin da aka kira kuri’ar murya a zaman na Alhamis, yan majalisar da suka ce a’a sun shafe muryar wadanda ke bukatar a cigaba da duba kudurin. Wannan na nufin an yi fatali da neman kara wa’adin zababbun shugabannin siyasa a kasar nan, kamar yadda aka yi a baya.
Da yake an yi watsi da kudurin, ba za a yi canji ga tsarin wa’adin mulkin Najeriya ba a halin yanzu. Shugaban kasa, gwamnoni, da shugabannin kananan hukumomi za su ci gaba da yin wa’adi na shekara hudu, tare da damar yin wa’adi na biyu.