Magidanta a Gombe Na Tserewa, Sun Bar Iyalansu da Matsaloli

Hukumar kare hakkin dan adam ta kasa (NHRC) ta bayyana cewa rahotanni 339 na cin zarafin hakkin dan adam sun shigo daga jihar Gombe. Mafi yawan rahotannin sun shafi rashin kulawar maza ga iyalansu, inda aka yi zargin cewa maza suna tserewa daga gida suna barin matansu da ‘ya’yansu cikin talauci.

Malam Ali Alola-Alfinti, kakakin hukumar NHRC, ya bayyana cewa yawaitar wannan matsala na faruwa ne sakamakon matsin tattalin arziki da jama’a ke fuskanta. A cikin rahoton, an nuna cewa kashi 50 na rahotannin sun shafi cin amanar iyaye, wanda ya nuna yadda maza ke barin iyalansu ba tare da abinci, tufafi, ko muhalli ba.

NHRC ta yi kira ga jama’a da su bayar da rahoto kan dukkanin cin zarafin da suke fuskanta, yana mai cewa shiru na jawo cikas a kokarin kare hakkin dan adam. Ali ya ce hukumar na gudanar da tarurruka da kungiyoyi masu zaman kansu da shugabannin al’umma don wayar da kan jama’a kan hakkin iyaye da kula da iyalansu.

Wannan lamari na nuna babban kalubale da ke fuskantar al’umma a Gombe, inda hukumar ke fatan magance wannan matsala ta hanyar ilimantar da maza kan muhimmancin zama tare da iyalansu da kuma daukar nauyin su.