Likitoci a Abuja Sun Bayyana Barazanar Yajin Aiki

Kungiyar Likitoci ta ARD-FCTA ta yi wa ministan Abuja, Nyesom Wike, barazanar tsunduma yajin aiki mafi muni idan ba a biya bukatunsu ba cikin mako biyu. Wannan barazanar ta biyo bayan taron da suka gudanar, inda suka bayyana damuwarsu game da rashin kyakkyawar kulawa da aka nuna musu.

Shugaban kungiyar, Dakta George Ebong, ya bayyana cewa likitoci suna bukatar a biya albashin watanni shida da aka rikewa ‘ya’yansu da aka dauka aiki a shekarar 2023, da kuma kudin horar da likitoci na shekara ta 2024. Haka zalika, sun nemi a gyara dokar ‘bonding’ daga shekara shida zuwa biyu.

A cewar Dakta Ebong, rashin adalcin da ake yi musu na iya rushe tsarin kiwon lafiya a Najeriya. Ya yi kira ga Wike da ya gaggauta daukar mataki kan bukatunsu, ko kuma su tsunduma yajin aikin da zai iya haifar da asarar rayuka a asibitocin Abuja.

Kungiyar ta kuma bukaci a tabbatar da cewa an biya kudin kayan aiki na 2024 da kuma kudin hadari na wata 13 na shekarar 2023. Sun bayyana cewa, idan ba a dauki mataki ba, yajin aikin na iya zama babbar barazana ga lafiyar al’umma.

Dakta Ebong ya tabbatar da cewa likitoci suna cikin hali na rashin jin dadi, inda ya fadi cewa, “Yayin da minista ke gyara gine-gine, ya kamata a kula da walwalar likitoci da ma’aikatan lafiya.”

Kungiyar likitocin ta yi kira ga al’umma da su fahimci cewa wannan yajin aiki na iya haifar da mummunan tasiri ga aikin kiwon lafiya a Abuja.