
Jami’an hukumomin tsaro na DSS sun kama shahararren mai barkwanci, Ɗan Bello, a filin jirgin sama na Kano. Wannan lamari ya jawo ce-ce-ku-ce mai karfi a tsakanin fasinjoji da ma’aikatan filin jirgin.
Ɗan Bello ya bayyana cewa, bayan isowarsa Najeriya, jami’an sun karɓi fasfonsa da kayansa, kafin su tafi da shi. Duk da haka, ya sanar da duniya cewa bai yi mamakin kame shi ba, yana kira ga jama’a da su kwantar da hankali, yana cikin koshin lafiya.
A yayin wata tattaunawa da jaridar DCL Hausa, Ɗan Bello ya bayyana cewa, “Dana sauko wasu mutane wanda kana ganinsu ka san hukumomi ne suka karɓi fasfo da sauran kayayyakina.” Ya kuma yi bayani kan tattaunawar da aka yi a cikin turanci kafin a sake shi.
Bayan kusan awa ɗaya da rabi na tattaunawa, an sake shi ba tare da bayani a hukumance ba kan dalilin da ya sa aka kama shi. Wata majiya ta tabbatar da cewa DSS ne suka kama shi, amma daga baya suka sake shi, suna iya samun sabbin umarni.
Ɗan Bello ya nuna cewa yana sane da yanayin Najeriya, yana mai cewa, “A Najeriya muke. Har da kayan gidan yarina na taho a shirye, ban yi mamakin kama ni ba.” Ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da kwanciyar hankali da fatan samun zaman lafiya.
Wannan lamari ya jawo sha’awar mutane da dama, musamman ma a Arewa, inda Ɗan Bello ya shahara wajen wallafa barkwanci da ke taɓa siyasa da zamantakewa. Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, DSS ba ta fitar da wata sanarwa ba kan wannan lamari.