
Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC, ta fara binciken jam’iyyar NNPP kan halaccin kudin yakin neman zaben 2023. Ana zargin wannan binciken da nufin rage karfin jagoran jam’iyyar, Rabiu Kwankwaso, musamman a zaben 2027.
Wannan bincike ya biyo bayan caccakar da Kwankwaso ya yi ga gwamnatin Bola Tinubu, inda ya zargi gwamnatin na mulkin mallaka a yankin Arewa. Kwankwaso ya bayyana cewa akwai shirin yi wa Arewa mulkin mallaka da Lagos ke yi, wanda hakan zai hana su ikon gudanar da harkokin su.
Wata majiya ta bayyana cewa hukumar EFCC ta fara binciken ne bayan korafi daga wasu fusatattun ‘yan jam’iyyar NNPP da aka kora. An umarci hukumar ta binciki Kwankwaso kan kudin kamfen na zaben 2023, tare da bukatar ya amsa tambayoyi.
Shugaban jam’iyyar NNPP ya zargi Tinubu da kokarin durkusar da jam’iyyar sa, yana mai cewa wannan na iya zama wani yunkuri na rufe bakin yan adawa a Najeriya. Ya kuma bayyana cewa akwai bukatar a duba wannan lamari da kyau, ganin yadda al’amuran ke gudana a siyasar Najeriya.
Karamin ministan gidaje da raya birane, Hon. Yusuf Abdullahi Ata, ya yi martani kan kalaman Kwankwaso, yana mai kira ga shugaban jam’iyyar NNPP da ya guji yin kalaman da zasu iya kawo tashin hankali a yankin.
Ana sa ran wannan bincike zai ja hankalin masu ruwa da tsaki a siyasa, musamman ma a lokacin da Najeriya ke shirin gudanar da zabe a 2027.