
A wata babbar katafaren taro da aka gudanar a Jihar Kano, kungiyar Arewa Youth Democratic Movement ta karrama Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da lambar yabo a matsayin jagoran da ya fi bayar da gudunmawa a bana. Wannan karramawa ta zo ne bayan irin kokarin da Kwankwaso ya yi wajen tallafawa matasa da kuma ci gaban al’umma.
Shugaban kungiyar, Muhammad Sabo Bakin Zuwo, ya bayyana cewa Kwankwaso ya cancanci wannan yabo saboda irin gudunmawar da yake bayarwa a fannoni da dama, musamman a bangaren ilimi da sana’o’i. Ya ce, “Sanata Kwankwaso jagora ne wanda ya taka rawar gani wajen bunkasa rayuwar matasa a Najeriya.”
Bayan bayar da wannan lambar yabo, jama’a da dama sun bayyana ra’ayoyinsu kan cancantar Kwankwaso, inda wasu suka yi imanin cewa zai iya zama shugaban Najeriya a zaben 2027. Wani mai suna Mohd Sidi ya rubuta a shafinsa na sada zumunta cewa, “Muna taya jagora murna. In sha Allahu, shugaban kasa ne na 2027.”
Masoyan Kwankwaso sun yi murnar wannan karramawa, suna masa addu’a da fatan samun nasara a zabe mai zuwa. Wani mai goyon bayan Kwankwaso, Shafiu Abdullahi, ya ce, “Duk wani abu da jagora ya karɓa, tabbas ya cancanta.”
Ana sa ran wannan lambar yabo za ta kara zaburar da Kwankwaso kan ci gaba da aikace-aikacen da zasu amfanar da jama’a, musamman matasa. Wannan karramawa ta nuna kyakkyawar sha’awa da goyon bayan da Kwankwaso ke da shi a tsakanin al’umma, tare da fatan cewa zai ci gaba da inganta rayuwar matasa da Najeriya baki daya.