Kwamitin Binciken Gobarar Tankar Fetur a Jigawa Ya Mika Rahotonsa ga Gwamnati

Daga Jigawa – gwamnatin Jigawa ta karbi rahoton kwamitin da ta kafa domin binciken faduwar tankar fetur da ta faru a jihar, wanda ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dama. Shugaban kwamitin, DIG Hafiz Muhammad Inuwa mai ritaya, ya bayyana cewa rahoton ya kunshi shawarwari masu muhimmanci da za su taimaka wajen kare rayuka a nan gaba.

A cikin rahoton, an bayyana cewa mutane 209 ne suka rasu a hadarin da ya faru a kauyen Majiya, karamar hukumar Taura. Har yanzu, mutane 38 na kwance a asibiti, yayin da mutane 86 suka samu sauƙi kuma sun koma gida.

DIG Inuwa ya sanar da cewa kwamitin ya bayar da shawarwari da suka haɗa da tabbatar da cewa tankokin fetur suna dauke da kayan kariya da za su hana mai zubewa idan an fadi tanka. Ya ce, binciken ya nuna cewa wasu motocin dakon mai ba su da kayan kariya, wanda ya ƙara ta’azzara hadarin.

Kwamitin ya kuma ba da shawarar samar da wuraren agaji na gaggawa da kuma gina hukumar kula da sufuri domin inganta tsaro a yankin. Gwamnan jihar, Umar Namadi, ya tabbatar da cewa zai yi amfani da dukkan shawarwarin da kwamitin ya bayar don inganta tsaro da kare rayukan al’umma.

Wannan hadari na tankar fetur ya jawo fargaba a tsakanin mazauna jihar, musamman ma bayan faduwar wannan tankar da ta yi sanadiyyar asarar rayuka sama da 200 a wannan lokaci. Hukumomi na ci gaba da daukar matakan gaggawa domin guje wa faruwar irin wannan lamari a nan gaba.