
Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS) ta sanar da cewa za ta gurfanar da Dan Bello a kotu bisa zargin da ya yi wa shugabanta, Sheikh Abdullahi Bala Lau, na bata sunan kungiyar.
Izala ta musanta zargin da Dan Bello ya yi cewa ta karɓi kuɗi daga gwamnatin tarayya don gina ajujuwa, tana mai cewa ayyukan suna karkashin masu wakiltar majalisar tarayya.
A cikin sanarwar da kungiyar ta fitar a shafinta na Facebook, ta bayyana cewa gine-ginen da ake magana a kansu suna daga cikin ayyukan wakilan majalisar tarayya, ba kuɗin da aka bai wa kungiyar ba.
Kungiyar ta ce Dan Bello ya yi kuskure wajen fassara bayanan ayyukan gine-ginen da wasu ‘yan majalisa suka shirya, kuma ta bukaci cewa ya fitar da hujjojin da ke goyon bayan zarginsa.
Haka zalika, Izala ta ce duk zarge-zargen da Dan Bello ke yi suna nuni da yunkurin bata sunan shugabanta da kungiyar, wanda ba tare da wata hujja ba ne.
Yanzu dai kungiyar ta bayyana cewa za ta gurfanar da Dan Bello a kotu domin kare martabar shugabanta da kungiyar. Za mu ci gaba da bibiyar wannan al’amari don ganin yadda shari’ar za ta kaya.