Kudirin Harajin Tinubu: Kwamitin Majalisa Zai Zauna da Babban Lauyan Gwamnati

Majalisar dattawa ta dakatar da ci gaba da muhawara a kan kudirin harajin Tinubu, bayan samun sukar daga fannoni daban-daban. Wannan mataki ya biyo bayan kafa kwamitin da zai duba matsalolin da ake kuka da su a kudirin harajin.

Kwamitin zai fara ganawa da babban lauya na kasa, Lateef Fagbemi SAN, domin tattauna batutuwan da suka shafi kudirin. Duk da haka, rahotanni sun nuna cewa babban lauyan ba ya cikin kasar nan, amma hakan ba zai hana zaman kwamitin ba.

Sanata Barau I Jibrin ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa kwamitin da aka kafa zai yi aiki tare da bangaren zartarwa domin magance koken jama’a. Shugaban kwamitin, Abba Moro, ya ce watakila ba za su gana da Lateef Fagbemi ba, amma ‘yan majalisar za su taru domin tattauna yadda za a ci gaba.

Wannan tsari na kwamitin yana da nufin duba korafe-korafen da jama’a suka yi game da kudirin harajin, wanda wasu ke ganin zai iya cutar da arewacin Najeriya.