Ku Mallaki Bitcoin: Hanyar Bunkasa Tattalin Arzikin Najeriya

Hanu Agbodje, wani masanin fasahar kere-kere, ya bayyana cewa Najeriya na bukatar mallakar Bitcoin domin bunkasa tattalin arzikinta ta hanyar cryptocurrency. A cewarsa, wannan mataki zai ba Najeriya damar shiga cikin manyan kasashen da ke amfani da kudin intanet.

Agbodje ya bayyana cewa, darajar Bitcoin ta karu da kashi 116% a shekarar da ta gabata, yayin da ake hasashen zai kai dala $180,000 kafin karshen 2025. Ya kawo misalin kasar El Salvador, wanda ta samu nasara ta hanyar sanya Bitcoin a matsayin kudi a dokance, wanda ya karfafa yawon bude ido da tattalin arziki.

A cewar rahoton Chainalysis, kimanin kashi 33% na al’ummar Najeriya suna zuba jari a cryptocurrency, wanda hakan ya sa Najeriya ta kasance a matsayi na biyu a duniya bayan Indiya. Hanu Agbodje ya ce akwai bukatar gwamnati ta kafa wata lalitar ajiya domin mallakar Bitcoin, irin yadda ake da lalitar ajiyar zinare da dala.

Agbodje ya yi hasashen cewa, a shekarar 2025, kasuwar cryptocurrency a Najeriya za ta kara girma, musamman saboda dawowar Donald Trump kan mulki a Amurka, wanda zai haifar da dokoki da kirkirar sabbin sulallan crypto.

Masani ya bayyana cewa, Najeriya na bukatar jan ragamar wannan fanni domin tabbatar da ci gaban tattalin arziki da kuma samun kudaden shiga daga kasashen waje. Ya kuma jaddada cewa wannan shekarar za ta yi tasiri a hada-hadar kudin intanet, tare da zuba jari a harkar cryptocurrency.