
A wani mataki mai cike da cece-kuce, kotun manyan laifuffuka ta duniya (ICC) ta ba da sammacin cafke Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, da tsohon ministan tsaron kasar, da kuma wasu kwamandojin kungiyar Hamas.
Wannan mataki ya biyo bayan cigaba da zubar da jini da ake yi a Gabas ta Tsakiya tsakanin Isra’ila da Hamas tsawon lokaci. Kotun ta ce ta gaji da rikicin da ke kawo asarar rayuka da dukiyoyi, kuma ta yanke shawarar daukar mataki domin dakile shi.
Wannan mataki da kotun ICC ta dauka ya jawo cece-kuce da suka daban-daban, inda wasu ke ganin yana da kyau domin kawo karshen rikicin, yayin da wasu ke ganin ba zai haifar da wani sakamako mai kyau ba.
Kotun ta ce tayi Watsi da yunkurin isra’ila na kalubalantar iKon da Kotun ke da shi kan sauraron shari’ar
Akwai bukatar a samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Gabas ta Tsakiya domin ci gaban yankin da duniya baki daya.
Domin haka a ci gaba da yin addu’a da fatan alheri domin kawo karshen rikicin a Gabas ta Tsakiya da duniya baki daya