
Wata kotu a ƙasar Iran ta yanke hukuncin kisa ga fitaccen mawaki, Amir Hossein Maghsoudloo, wanda aka fi sani da Tataloo, bisa zargin taɓa mutuncin Annabi Muhammad (S.A.W). An yankewa mawakin hukuncin ne bayan an kama shi da laifin ɓatanci ga Manzon Allah.
Kotun ta yanke hukuncin ne bayan hujjojin da aka gabatar, duk da cewa an fara masa hukuncin shekara biyar a gidan yari. Kotun kolin Iran ta soke wannan hukuncin na ɗaurin shekaru biyar saboda rashin gamsuwa da hukuncin.
Tataloo, wanda ya kasance yana zaune a Istanbul tun 2018, an miƙa shi ga hukumomin Iran a watan Disamba 2023 bayan ‘yan sandan Turkiyya sun kama shi. A ƙarin tuhumomin, an yanke masa hukuncin daurin shekaru 10 saboda laifin tallata karuwanci da kuma yada “farfaganda” a ƙasar Musulunci.
Mawakin mai shekaru 37, ya shahara a fagen waƙoƙin rap, pop, da R&B, kuma ya kasance cikin bincike na hukumomi saboda salon sa na rayuwa da zane-zanen da ke jawo hankalin matasa. Wannan hukuncin na kisa ya jawo ce-ce-ku-ce a duniya, inda ake ci gaba da tattaunawa game da hakkin ɗan adam da kuma addini a ƙasashen Musulmi.