
Kotun daukaka kara da ke Ibadan ta yanke hukunci kan rigimar sarauta a jihar Oyo, wanda ya shafi kujerar Soun na Ogbomoso. Kotun ta tabbatar da nadin Oba Ghandi Olaoye, Orumogege III, a matsayin Soun na Ogbomoso bayan daukaka karar da ya shigar.
A ranar 25 ga Oktoba, 2023, kotun Oyo ta soke nadin Oba Ghandi, tana mai cewa an yi nadin ba bisa ka’ida ba. Sai dai, a cikin hukuncin da Mai Shari’a Nimpar ya fitar, kotun daukaka kara ta watsi da wannan hukunci, ta tabbatar da cewa Oba Ghandi ya cancanci ci gaba da mulkinsa.
Hukuncin ya biyo bayan daukaka karar da Oba Ghandi ya shigar, inda kotun ta bayyana cewa dukkan dalilan da aka gabatar a cikin karar sun goyi bayan sa. Hakan na nuni da cewa an bi dukkan ka’idojin da suka dace wajen nadin sa.
A gefe guda, rigimar sarautar ta dauki sabon salo lokacin da dan sarki, Ismaila Owoade, ya garzaya kotu, yana neman a soke nadin Prince Abimbola Owoade a matsayin Alaafin na Oyo. Wannan ya jawo cece-kuce a cikin al’umma, yayin da kotun ta sanya ranar 11 ga Maris, 2025, don sauraron karar.
Kotun ta bayyana cewa akwai bukatar a bi ka’idodin doka wajen nadin sarakuna domin tabbatar da zaman lafiyar al’umma. Wannan hukunci na kotu ya dawo da kwanciyar hankali a cikin al’ummar Ogbomoso, yayin da Oba Ghandi Olaoye ya ci gaba da gudanar da al’amuransa a matsayin sarki.