
A cikin wani jawabi mai karfi, Sheikh Lawan Abubakar Triumph ya roki Sarki Aminu Ado Bayero da ya janye shirin hawan sallah da ke tunkarar Kano, domin guje wa rikice-rikicen da ka iya tasowa. Malamin addinin ya bayyana cewa, lamarin na da matukar hatsari ga zaman lafiya a jihar.
A lokacin tafsirin Ramadan, Sheikh Triumph ya bayyana cewa akwai barazana ga al’umma, kuma ya kira ga kowa da ya yi tunani mai zurfi akan wannan al’amari. Ya yi nuni da cewa, duk wanda ke da hankali zai fahimci cewa a halin yanzu, Kano na fuskantar babban kalubale.
Malamin ya bayyana cewa, gwamnatin Kano ta ba Sarki Muhammadu Sanusi II umarnin gudanar da hawan sallah, yayin da Sarki Aminu Ado ya sanar da hukumomi cewa shima zai fito hawan sallah. Wannan yanayi na haifar da rudani tsakanin bangarorin biyu.
Sheikh Triumph ya yi kira ga Sarki Aminu da ya duba girman Allah ya janye wannan shiri, domin an san shi da soyayya da zaman lafiya. Ya ce, “Muna rokon alfarma ga ɓangaren mai martaba Sarki Aminu su dubi Allah su tsare jinin al’umma.”
Haka zalika, ya yi gargadi cewa, idan an ci gaba da wannan shiri, hakan na iya jawo tashin hankali a Kano. Wannan kira na Sheikh Triumph ya zo a lokacin da ake ta fama da rikicin sarauta a masarautar Kano.