Kin Biyan Haraji Babbar Matsala Ce A Abuja

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana kin biyan haraji a matsayin babbar matsalar da yake fuskanta a Abuja.  Wike ya bayyana hakan ne yayin da yake duba wasu ayyukan raya kasa da gwamnatin tarayya ke gudanarwa a babban birnin, wadanda aka shirya kaddamarwa yayin bikin cika shekaru biyu da Shugaba Bola Tinubu ya yi kan karagar mulki.

Daga cikin ayyukan da ministan ya duba har da Cibiyar Taro ta Kasa (AICC) da kuma fadada titin Obafemi Awolowo (N5) daga Life Camp zuwa Ring Road III.  Sauran sun hada da gadoji da tituna da aka kammala a NICON Junction, gidajen alkalai, da kuma titin Wole Soyinka.

Wike ya koka da yadda mazauna Abuja ke kin biyan haraji duk da irin kokarin da gwamnati ke yi na samar musu da ababen more rayuwa. Ya ce, “Mutane suna son ganin kyawawan abubuwa, amma ba sa son sanin daga ina kudin yake fitowa.”

Ministan ya kuma caccaki masu hannu da shuni da suke da gidaje a kasashen waje, wadanda ke biyan haraji a can amma suna kin biya a Najeriya. Ya ce, “A nan gida ba kowa ke son bin doka ba, saboda kowa na tunanin ba za a hukunta shi ba.”

Wike ya jaddada cewa FCT ba ta cikin jihohin da ke samun kason kudin shigar man fetur, don haka haraji shi ne babbar hanyar samun kudin shiga. Ya bayyana cewa yawancin masu gidaje da filaye a Abuja ba su biya harajin kasa ba tsawon shekaru 30, kuma gwamnati na duba yiwuwar kara kudin harajin domin daidaita shi da halin da ake ciki a yanzu.

Dangane da wa’adin makonni biyu da Shugaba Tinubu ya bayar ga wadanda ake bin bashi, Wike ya ce babu wata barazana da za ta hana gwamnati daukar matakin da ya dace. Ya ce, “Kar kowa ya yi zaton barazana zai hana mu aiki. Za mu yi abin da ya dace, domin wannan shugabanci ne, hakkinmu ne mu yi abin da ya dace.”  Ya kuma gargadi cewa duk wanda ya ki biyan bashin haraji, gwamnati za ta kwace kadarorinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *