
Kasuwar hannun jari ta Najeriya (NGX) ta fuskanci asarar Naira tiriliyan 1.4 a cikin makonni hudu, wanda ya sa jimillar jarin kamfanoni ya ragu zuwa Naira tiriliyan 65.819. Ma’aunin hannun jari na ASI ya ragu da kashi 2.7%, yana nuna ci gaba da faduwar kasuwa duk da saukar farashin kayayyaki a Najeriya.
A ƙarshen ranar Juma’a, jimillar jarin kamfanonin da aka yi hada-hadarsu ya ragu daga Naira tiriliyan 67.193 zuwa Naira tiriliyan 65.819, daidai da ragin kashi 2.1. Masu saka hannun jari suna fuskantar fargabar lalacewar kudaden su, yayin da masana ke ganin wannan babbar dama ce ta sayen hannun jari a farashi mai sauki.
Kasuwar ta ragu sosai, inda jimillar hannun jarin da aka sayar a mako ya sauka da kashi 11.5% zuwa Naira biliyan 2.90. Jimillar kuɗin da aka samu a hada-hada ya ragu da kashi 24.3%, sakamakon ƙauracewar masu zuba jari.
Daga cikin manyan bangarorin da suka tafka asara, biyar sun fuskanci hasara, yayin da bangaren kayan masarufi kadai ya samu ɗan ci gaba. Masana sun bayyana cewa wannan koma bayan ya samo asali ne daga fargabar da masu saka jari ke yi kan ribar kamfanoni da matsin tattalin arziki.
Duk da haka, masana suna ganin wannan babbar dama ce ga masu saka hannun jari na dogon lokaci domin sayen hannun jari a farashi mai sauki, suna shawarci su yi nazari kan manyan kamfanonin hannayen jari da ke ba da riba.