
A cikin ‘yan makonnin da suka gabata, kasashen Afirka da dama sun dauki matakan raba gari da sojojin ƙasar Faransa a cikin al’amuran tsaro. Wannan mataki ya biyo bayan gagarumin rashin jin dadi da aka nuna game da tasirin Faransa a harkokin cikin gida na kasashen.
Hedkwatar rundunar sojin Najeriya ta musanta jita-jitar cewa za a kafa sansanin sojojin Faransa a Najeriya, inda ta ce wannan labari ba shi da tushe. Duk da haka, wasu kasashen Afirka sun yi matukar tsayawa kan wannan batu.
Jerin Kasashen da Suka Katse Alaka
1. **Nijar**: Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta yanke duk wata alaka da taimakon soji daga Faransa a 2023. Sojojin da suka karɓi mulki sun kori jakadan Faransa da ke Nijar, lamarin da ya jawo damuwa daga gwamnatin Faransa.
2. **Chadi**: Chadi ta kawo karshen yarjejeniyar haɗin gwiwa ta tsaro da Faransa, bayan shekaru 60 da samun ‘yancin kai. Wannan matakin ya jaddada burin Chadi na tabbatar da ‘yancin kai da daidaita kawancenta da sauran kasashen duniya.
3. **Gabon**: A watan Agustan 2023, sojojin Gabon suka kwace mulki, inda suka dakatar da hadin gwiwar soji da Faransa bayan juyin mulkin.
4. **Mali**: Kawancen sojin Mali da Faransa ya rushe bayan juyin mulkin da ya faru a shekarun 2020 da 2021. Mali ta kori jakadan Faransa, wanda ya sa Faransa ta janye sojojinta daga ƙasar.
5. **Senegal**: Shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya bayar da umarnin rufe sansanonin sojin Faransa a kasar, yana mai jaddada cewa wannan matakin yana da alaka da ‘yancin Senegal.
6. **Burkina Faso**: Gwamnatin sojin Burkina Faso ta kori sojojin Faransa bayan sun fice daga Mali, inda aka ba su wa’adin makonni huɗu su bar ƙasar.
Wannan jiri na yanke alaka da sojojin Faransa na nuna ƙoƙarin kasashen Afirka na samun ‘yancin kai da kuma rage tasirin mulkin mallaka. Wannan al’amari na jawo hankalin kasashen duniya, yayin da kasashen Afirka ke neman hanyoyin da zasu inganta tsaronsu da ci gaban su.