
A ranar Asabar, 23 ga watan Nuwamba, 2024, za a bude kasuwar baje koli ta duniya a Kano, inda tuni kamfanoni su ka shirya halartar gagarumin taron. Cibiyar bunkasa ciniki da masana’antu da ma’adinai da ayyukan gona a jihar (KACCIMA), ta bayyana cewa shirye-shirye sun kammala domin tabbatar da taro mai inganci.
Ana sa ran kamfanoni daga ciki da wajen Najeriya ne za su hallara a kasuwar domin baje hajarsu ga masu sha’awa. Kamfanonin sun hada da kasar India da na Nijar, yayin da aka tsara cewa kowa zai iya shiga bajekolin kyauta.
Shugaban KACCIMA, Garba Imam ya fadi cewa akalla kamfanoni 300 ne aka da tabbacin za su halarci kasuwar baje koli. Ya kara da cewa kamfanonin sun hada da na cikin Najeriya da kasashen waje kamar su India da Nijar.
Alhaji Garba Imam ya bayyanacewa za a iya shiga baje kolin kyauta domin ba jama’a damar shiga kasuwar ba tare da wata matsala ba. Za a gudanar da baje kolin karo na 45 na kwanaki akalla 15, daga 23 Nuwamba, 2024 zuwa 7 Disamba, 2024 domin ba al’umma damar shiga kasuwar.
Ana sa ran Kano za ta cika makil da yan kasuwa yayin da za a fara bikin baje koli karo na 45 a ranar Asabar.