
Kakakin majalisar Borno, Rt. Hon. Abdulkarim Lawan, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kafa birgediyar soja a kananan hukumomin Guzamala da Kukawa. Wannan kira ya biyo bayan mummunan hali da garuruwan biyu ke fuskanta, inda Boko Haram ke ci gaba da mamaye yankin.
Shugaban majalisar ya bayyana cewa fiye da shekaru goma ne Boko Haram suke cin karensu a Guzamala da Kukawa, tare da jaddada cewa babu farar hula ko na soja a wurin. Ya ce akwai bukatar samar da rundunar soji domin ‘yantar da yankin daga hannun ‘yan ta’adda.
Lawal ya yi bayani cewa akwai bukatar a tura sojoji masu yawa, tare da kayan aiki masu inganci, domin dawo da tsaro a wannan yanki. Haka zalika, ya roki gwamnatin tarayya da ta taimaka wajen dawo da ‘yan gudun hijira zuwa gidajensu.
Duk da haka, ya yaba wa Gwamna Babagana Zulum bisa kokarin da ya ke yi na farfaɗo da al’ummomin da suka tsere daga Boko Haram, amma ya bayyana cewa har yanzu akwai kalubale da dama da suka shafi tsaro a jihar Borno.