
A yau, Talata 17 ga watan Disamba, 2024, tsohon shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya cika shekaru 82 a duniya. Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya taya Buhari murnar wannan rana ta musamman tare da yi masa fatan karin lafiya da kwanciyar hankali.
Jonathan ya bayyana cewa yana yaba wa Buhari kan cigaban da ya kawo wa Najeriya a lokacin mulkinsa. A cikin sakon taya murnar da ya fitar, Jonathan ya bayyana:
“A madadin ni da iyalaina, ina mika sakon taya murna gare ka a wannan rana ta musamman. Ina addu’a Allah ya ba ka lafiya, hikima da farin ciki.”
Hakanan, Jonathan ya jaddada cewa yana fatan sabuwar shekara a rayuwar Buhari za ta kara kusanci tsakaninsa da masoyansa, yana mai fatan ranar haihuwarsa ta kasance cike da kauna da farin ciki.
Wannan sakon na Jonathan ya nuna alamar hadin kai da girmama juna tsakanin tsofaffin shugabannin Najeriya, wanda ke da nufin inganta zaman lafiya da hadin kan al’umma.