
Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ya sake komawa kan batun zaɓen shekarar 2015, inda ya bayyana cewa na’urar tantance katin zaɓe da hukumar INEC ta gabatar a lokacin ta haifar da matsaloli da suka kusa haddasa rikici a Najeriya. Jonathan ya bayyana wannan a cikin wani taro da ƙungiyar YIAGA Africa ta shirya a Abuja.
A cewarsa, na’urar ta ƙi karɓar katin zaɓe na shi da na iyalansa, wanda hakan ya jawo damuwa a tsakanin masu kada kuri’a. Ya ce, “Lokacin da Jega ke rike da INEC, na’urar ta ƙi karɓa, ta kuma kusa haddasa rikici a ƙasa.” Jonathan ya bayyana cewa wannan lamari na nuna yadda tsarin zaɓe ke da tasiri ga zaman lafiya a ƙasar.
Tsohon shugaban ya jaddada cewa nasarar kowanne zaɓe na da alaƙa da yadda hukumar zabe da ƴan sanda suka gudanar da shi. Ya ce, “Zaman lafiyar kowacce dimokuradiyya na da alaƙa da yadda ake gudanar da zaɓe da kuma kula da tsaronsa.”
Jonathan ya yabi matasan Najeriya kan yadda suke ƙara taka rawa a harkar zaɓe, yana mai cewa wannan yana da matuƙar muhimmanci ga ci gaban ƙasar. Duk da kalubalen da aka fuskanta a zaɓen 2015, tsohon shugaban ya bayyana cewa yana da kyau a ci gaba da amfani da fasahar zamani a harkokin zaɓe domin inganta tsarin dimokuradiyya a Najeriya.