Jihar Kaduna Ta Kafa Tarihi a Fannin Noman Inabi a Najeriya

A ranar Talata, 21 ga Janairu, 2025, shugaban ƙungiyar manoman inabi ta ƙasa, Abdullah Dalhatu, ya bayyana cewa jihar Kaduna ta zama babbar mai samar da inabi a Najeriya. Wannan sanarwa ta biyo bayan ziyara da ya kai tare da shugaban karamar hukumar Kudan, Dauda Iliya Abba, zuwa wata gonar inabi mai girman kadada biyar a yankin.

Rahotanni sun nuna cewa karamar hukumar Kudan tana samar da kusan kashi 85% na inabin da ake nomawa a Najeriya. A watan Janairu na wannan shekara, wata gonar inabi a Kudan ta samar da tan 22 na inabi wanda aka fitar zuwa sassan ƙasar.

Dalhatu ya bayyana cewa yanayi mai kyau da kasa mai kyau a Arewacin Najeriya, musamman a Kudan, sun zama ginshikan nasarar noman inabi a wannan yanki. Ya kuma jaddada cewa gonakin inabi a Kudan suna da damar samar da nau’ikan inabi masu yawa, wanda ke da tsawon rai har na shekaru 50.

Haka zalika, shugaban karamar hukumar Kudan, Dauda Iliya Abba, ya yaba wa jajircewar manoman yankin wajen zama gaba a harkar noma inabi. Ya bayyana cewa noma a jihar Kaduna yana da matuƙar tasiri wajen habaka tattalin arziki da bunƙasa yankuna, musamman a karamar hukumar Kudan.

A cikin sharhi kan wannan ci gaba, mutane da dama a kafafen sada zumunta sun bayyana jin dadinsu da wannan nasara, suna mai cewa noma inabi zai zama babbar hanya ga samun kuɗin shiga ga manoma da gwamnati idan aka mai da hankali a kansa. Shugaban ƙaramar hukumar ya tabbatar da cewa gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, yana da shirin tallafawa noma a jihar domin tabbatar da cigaban tattalin arziki.