Jigon PDP Ya Bayyana Shirin Fitar da Tinubu Daga Aso Rock a 2027

Kakakin matasan jam’iyyar PDP na kasa, Dare Glintstone Akinniyi, ya bayyana cewa jam’iyyar PDP tana da shirin fitar da Bola Tinubu daga Aso Rock a shekarar 2027. A wata tattaunawa da aka yi da manema labarai, Akinniyi ya ce PDP ita ce kadai jam’iyyar da ke da ikon kawar da APC daga mulki.

Akinniyi ya yi ikirarin cewa APC jam’iyya ce da ta gaza wajen gudanar da mulki, inda ba ta da shiri ko dabarar kawo ci gaba a Najeriya. Ya ce, “A shekarar 2025, ‘yan Najeriya su shirya ganin yadda PDP za ta yi adawa mai karfi da APC.”

Ya jaddada cewa PDP tana da bukatar gyara da tsabtace cikin gidanta domin samun nasara a zaben 2027. A cewarsa, “Duk da cewa jam’iyyar tana cikin rikici yanzu, za ta dawo da tasirinta a shekarar 2025.”

Akinniyi ya kuma bayyana cewa PDP za ta yi aiki tare da ‘yan Najeriya don tabbatar da cewa APC ta fice daga Aso Villa. Ya ce, “Muna ganin cewa PDP za ta zama madadin wannan jam’iyya da ta nuna gazawarta a mulki.”