
Kasashe da dama suna da hukumomin tsaro na sojoji da ‘yan sanda, amma akwai wasu ƙasashe guda biyar da ba su da waɗannan hukumomi. Ga jerin waɗannan ƙasashen:
1. Iceland
Iceland tana daga cikin ƙasashen da ba su da sojoji. Tana da yawan mutane 383,726 a farkon shekarar 2024. Ƙasar tana dogara da ƙungiyar NATO da ƙawancen da take da shi da Amurka domin samun kariya.
2. Liechtenstein
Liechtenstein ƙaramar ƙasa ce da ke a tsakanin Switzerland da Austria. Ta soke sojojinta a shekarar 1868 saboda tsadar kula da su, kuma tana dogara ga Switzerland wajen samun taimako idan buƙatar hakan ta taso.
3. Vatican
Vatican ba ta da sojoji ko ‘yan sanda. Tana samun tsaro daga rundunar Swiss Guard, wacce ke kare Fafaroma. Hakanan, Vatican na dogara ga sojojin Italiya domin ƙara tsaro.
4. Monaco
Monaco, ƙaramar ƙasa da ke a gaɓar French Riviera, ba ta da sojoji. Tsaronta ya dogara ne akan Faransa, wacce ke da yarjejeniyar kare Monaco idan buƙatar hakan ta taso.
5. Andorra
Andorra tana a tsakanin Faransa da Spain, kuma ba ta da sojoji. Tana dogara ga Faransa da Spain domin samun kariya daga duk wata barazana.
Hanyoyin Tsaro
Kasashen da ba su da sojoji suna samun tsaro ta hanyoyi na musamman, kamar ƙawance da wasu ƙasashe, wanda ke ba su damar wanzar da zaman lafiya ba tare da jami’an tsaro na kansu ba. Yawancin waɗannan ƙasashen suna da ƙarancin aikata laifuka, wanda ke nuna ingancin zaman lafiyarsu.