Jam’iyyar SDP Ta Musanta Hadin Kai da APC a Tunkarar Zaɓen 2027

Adewole Adebayo, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar SDP a zaɓen 2023, ya bayyana cewa jam’iyyar ba ta shirya yin haɗaka da APC ko wata jam’iyya a gabanin zaɓen shekarar 2027. Wannan bayani ya fito ne a lokacin ganawa da shugabannin jam’iyyar na jihar Ogun a birnin Abeokuta.

Adebayo ya ce jam’iyyar SDP tana tsaye tsayin daka kan manufofinta, yana mai jaddada cewa suna maraba da duk wanda ke son shiga cikin jam’iyyar, amma ba tare da masu halayen banza ba. Ya musanta jita-jitar da ke cewa jam’iyyar su reshe ce ko ɓangare na APC, yana mai cewa, “Idan APC tana da cuta, to su je asibiti a yanke ta.”

Ya ƙara da cewa jam’iyyar SDP tana da kyakkyawan tarihin shugabanci tun daga shekarar 1989, kuma suna da manufar da ta dace da jin dadin al’ummar Najeriya. Adebayo ya yi nuni da cewa, “Mu jam’iyya ce mai ƙarfi. Mun fi kowace jam’iyyar da ake da ita daɗewa.”

A cikin wannan ganawar, yana tare da tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung, da kuma shugabannin jam’iyyar na Ogun, Oyo, da Legas. Adebayo ya bayyana cewa jam’iyyar ta shirya ta karɓi sababbin mambobi masu gaskiya, amma ba mutum masu alamar tambaya kan halayensu ba.

Wannan bayani na Adewole Adebayo ya jawo hankalin masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa, musamman ma a lokacin da ake tunkarar zabe mai zuwa.