Jam’iyyar Peter Obi ta Fara Shiri a Jihohi 36 domin Kawar da Tinubu a 2027

Jam’iyyar Labour (LP) ta kaddamar da shirin sake tsara tsarin jagorancin jihohi da kuma shirin tunkarar zaɓen 2027, a matsayin wani mataki na karfafa gwiwar jam’iyyar bayan kalubalen da suka fuskanta a zaɓen 2023.

A cikin sanarwar da jam’iyyar ta fitar, an bayyana cewa za a kafa kwamitin jagoranci a jihohi domin ƙarfafa alaƙa tsakanin shugabannin jam’iyyar da kungiyoyin sa-kai. Hakan zai haɗa da horar da sababbin mambobi da kuma shigar da su cikin tsarin jam’iyyar a matakai daban-daban.

Jam’iyyar LP ta ce za ta ƙaddamar da sabon tsarin shugabanci a hedkwatocin jam’iyyar a fadin Najeriya a ranar Juma’a. Wannan tsari yana nufin gina cibiyoyin jagoranci a jihohi da za su haɗa shugabannin gangami da wakilai, tare da ba su horo na musamman don gudanar da ayyukansu cikin nasara.

Hakanan, jam’iyyar ta bayyana cewa za ta tabbatar da cewa mambobin ƙungiyoyi suna da damar shiga jam’iyyar cikin sauƙi, inda za a tallafa musu wajen zama shugabanni ko wakilai a matakai daban-daban.

Wannan shiri na LP na tunkarar zaɓen 2027 yana da nufin ƙarfafa tsarin tafiyarta daga tushe da kuma samar da shugabancin da zai iya tunkarar kalubalen da suka shafi Najeriya a halin yanzu.